Yanzu-yanzu: Masoya Ramalan Yero sun mamaye kotu suna zanga-zanga

Yanzu-yanzu: Masoya Ramalan Yero sun mamaye kotu suna zanga-zanga

Ayarin magoya bayan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero sun mamaye harabar babban kotun tarayya da ke zaune a Kaduna yau Laraba, 6 ga watan Yuni, 2018.

Tsohon gwamnan na gurfana gaban kotun ne bisa ga zargin almundana da hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ke musu.

Zaku tuna cewa alkalin kotun, Jastis Muhammad Shua’aibu ya bada umurni a makon jiya cewa a garkame tsohon gwamnan da wasu 3 a kurkuku har ranan 6 ga watan Yuni.

An gurfanar da tsohon gwamnan ne tare da tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Abubakar Gaya Haruna; tsohon sakataren gwamnatin jihar, Hamza Ishaq, da tsohon ministan wuta, Nuhu Somo Wya.

Ana tuhumar Yero da laifin almundahanar kudi N700 million da kuma yaudara.

KU KARANTA: Duba hotunan wani magidanci da ya yiwa wata yarinya mai shekaru 5 fyade

Wannan abu ya jawo cece-kuce cikin al'umma wanda ya kai har malamin addini sun sanya baki cikin al'amarin.

Wani malamin addinin Musulunci mai ra’ayin rikau dake jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya zargi shugaba Buhari da kewaye kan sa da mashawarta marasa ilimi kuma marasa tausayi.

Gumi na wadannan kalamai a matsayin martini ga nuna hoton tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ramalan Mukhtar Yero, dauke da allon rubutun laifukan da ake tuhumar sa da su bayan hukumar EFCC ta gurfanar das hi gaban kotu ranar Alhamis da ta wuce.

Gumi ya bayyana cewar binciken da ake yiwa wasu tsofin gwamnoni a kasar nan, ra’ayin wasu masu bas hi shawara ne da basa tare da mutane.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel