An kama wani katon Allah yana shigar mata yana sana'ar karuwanci

An kama wani katon Allah yana shigar mata yana sana'ar karuwanci

Wani labari mai cike da al'ajabi da kuma ban haushi da ya riske mu shine na wani katon asara da aka kama a kasar Uganda ta nahiyar Afrika da yake badda-kama ta mata kuma yana sana'ar karuwanci domin ya yaudari maza ya ansar masu kudi kamar dai yadda ya fada da bakin sa.

Rahotannin da muka samu dai sun tabbatar mana da cewa dubun matashin ta cika ne yayin da yake yiwa wani namijin kwarkwasa yana so ya labbace shi a damfare shi ya ansar masa kudi.

An kama wani katon Allah yana shigar mata yana sana'ar karuwanci
An kama wani katon Allah yana shigar mata yana sana'ar karuwanci

An kama wani katon Allah yana shigar mata yana sana'ar karuwanci
An kama wani katon Allah yana shigar mata yana sana'ar karuwanci

KU KARANTA: Ku sadu da dan shekara 15 da yafi sa'annin sa tsawo a Najeriya

Legit.ng ta dai haka zalika ta samu cewa hotunan katon da ke ta yawo dai ko kusa ba su taba nuna cewa ba mace bace domin kuwa dukkan su yana sanye ne da kayan mata ya kuma caba kwalliya.

Wannan dai ba shine karo na farko ba da ake kama maza suna shigar mata domin wata manufa ta su ta daban a kasar ta Uganda da ma sauran kasashe da dama.

dan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel