Duk miji da matan da basu san lamban sirri na katin ATM din junansu ba toh ba ma’aurata bane – Mataimakin kwamishinan yan sanda
Mataimakin kwamishinan yan sanda, Abayomi Shogunle ya yi wani sharhi mai kayatarwa a shafinsa na sadarwa kwanan nan..
Babban jami’in dan sandan ya wallafa a shafinsa na twitter cewa duk wasu ma’aurata da basu san lambar sirri na katin ATM dinsu ba toh babu wani tasiri a zamansu.
Yace idan har ma’auratan basu son fadama juna lambar sirrin aiyarsu na banki, toh suyi addu’an Allah ya hada kowa da rabonsa na alkhairi.
Ya wallafa kamar haka: “Mata da mijin da basu san katin sirrin ATM din junansu ba toh har yanzu sunansu saurayi da budurwa.
KU KARANTA KUMA: An gano rishon Biliyan 9 da Jonathan ya saya bayan shekaru 3
“Tambayi abokan zamanku lamban sirrinsu yanzu. Idan yaki ko taki sanar da kai toh fara addu’an Allah ya hada ka/ki da rabonku na alkhairi.
“Amman banda sarayi da budurwa.”
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng