Dara ta ci gida: Mutane 10 sun Mutu sandiyyar arangama da ‘Yan kungiyar asiri su kayi

Dara ta ci gida: Mutane 10 sun Mutu sandiyyar arangama da ‘Yan kungiyar asiri su kayi

- Rikicin gungun wasu 'yan kungiyar asiri yabar baya da kura

- Yayin arangamar da suka yi Mutane sun sheka Lahira wasu kuma sun jikkata

- Sai dai kuma har yayi sanadiyyar Mutuwar wadanda basu ji ba ba su gani ba

A kalla Mutane 10 sun sheka lahira yayin da wasu da yawa suka jikka a dalili wata arangama da ta afku tsakanin wasu kungiyoyin asiri suka yi a Otukpo dake jihar Benue.

Dara ta ci gida: Mutane 10 sun Mutu sandiyyar arangama da ‘Yan kungiyar asiri su kayi
Dara ta ci gida: Mutane 10 sun Mutu sandiyyar arangama da ‘Yan kungiyar asiri su kayi

Rahotanni dai sun nuna cewa an yi wannan mummunar arangama ne da ta lakume rayuka har 10 a wata fitacciyar mashayar giya da tayi kaurin suna wato Banana Island.

Majiyarmu ta bayyana cewa daga cikin wadanda suka rasa rayukansu har da wani mai aski da ya fito wajen shagonsa harbi ya same shi akan Titin Akpa, yayin da wani ma iftila’in ya rutsa da shi a kusa Uloko lane duk a karamar hukumar Otukpo.

KU KARANTA: Maganar gaskiya shekaru 4 sun yi kadan da duk mai son ya kawo gyara a Najeriya - Osinbajo

Mazauna yankin dais un bazama domin tsira da rayukansu yayin da kayayyaki duk suke a warwatse.

Rigingimu dai tsakanin ‘yan kungiyoyin asiri ya sha faruwa kuma yana yawaita salwantar rayuka cikin sauki a duk sa’ilin da suka tafka rigima, a bisa haka ne hukumomi ke daukan tsauraran matakai kan wanda duk aka kama da hannu cikin aiyukan kungiyoyin asiri.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng