Wata bahaushiya, 'yar Kano ta musuluntar da baturen Amurka sannan ta aure shi

Wata bahaushiya, 'yar Kano ta musuluntar da baturen Amurka sannan ta aure shi

Wani labari mai ratsa zuciya da ya auku a garin Kano dake a shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya na nuni ne da yadda wata bahaushiyar 'yar asalin Kano din tayi gamo da katar bayan da ta musuluntar da wani baturen Amurka, ta kuma aure shi a karshen satin da ya gabata.

Kamar dai yadda muka samu daga labaran dake ta yaduwa a kafafen sadarwar zamani, ma'auratan na yanzu sun shafe kusan shekaru biyu suna ta zabga soyayyar su a kafar sadarwar zamani ba tare da haduwa da juna ba.

Wata bahaushiya, 'yar Kano ta musuluntar da baturen Amurka sannan ta aure shi
Wata bahaushiya, 'yar Kano ta musuluntar da baturen Amurka sannan ta aure shi

KU KARANTA: Masarautar Saudiyya ta mallakawa Yarima Bin Salman ikon Makka da Madina

Legit.ng ta samu cewa bayan sun gama daidaitawa da juna ne dai sai baturen ya nufo Najeriya inda ya sauka a garin Kano ya kuma aure matar sa a wani yanayi mai ban sha'awa da kayatarwa.

Da take karin haske, amaryar ta bayyana cewa tuni daman ita bata boye masa ba cewar ta taba yin aure har sau biyu sannan kuma tana da da amma duk da haka baturen ya amince ya aure ta.

Haka zalika dai ance baturen ya musulunta, yanzu ya canza suna ya zuwa Musa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel