Da dumin sa: Gwamnan Bauchi ya maye gurbin tsohon mataimakin sa da yayi murabus

Da dumin sa: Gwamnan Bauchi ya maye gurbin tsohon mataimakin sa da yayi murabus

Labarin da muke samu da dumin sa na nuni ne da cewa Gwamnan jihar Bauchi dake a shiyyar Arewa maso gabashin kasar nan Gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar ya nada Alhaji Audu Sule Katagum a matsayin sabon mataimakin sa.

Kamar dai yadda muka samu, Gwamnan ya bayyana wannan nadin ne lokacin da yake ganawa da wasu masu ruwa da tsaki a gwamnatin sa a gidan gwamnatin jihar.

Da dumin sa: Gwamnan Bauchi ya maye gurbin tsohon mataimakin sa da yayi murabus
Da dumin sa: Gwamnan Bauchi ya maye gurbin tsohon mataimakin sa da yayi murabus

KU KARANTA: Malamin addini ya lekowa Buhari faduwa a 2019

Legit.ng ta samu cewa shi dai Alhaji Audu Sule Katagum an nada shi ne domin ya maye gurbin tsohon mataimakin gwamnan Injiniya Nuhu Gidado da yayi murabus a watan jiya.

A wani labarin kuma, Babban jakadan kasar Ghana a Najeriya Mista Rashid Bawa ya nesanta kasar sa da kalaman da aka ruwaito wai cewa tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce shugaban kasar Ghana Nana Akuffo-Addo ne ya fada game da harkar tsaron Najeriya.

Da yake karin haske game da lamarin, jakadan kasar Ghana din ya fada a ranar Juma'ar da ta gabata cewa tsohon shugaban kasar ya datsi kalaman shugaban kasar ta Ghana ne amma ba haka yake nufi ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel