Kanjamau: Ashe karamar da tsohon shugaba Jammeh yake rabawa ta bogi ce

Kanjamau: Ashe karamar da tsohon shugaba Jammeh yake rabawa ta bogi ce

- A shekarun baya, shugaban Gambia Yahya JAmmeh yace yana warkas da kanjamau

- Yayi ikirarin karama saboda yana yawo da kur'ani a hannu ko'ina

- An kada shi zabe amma yaki yarda ya tafi saida Najeriya ta kai sojoji kasarsa

Kanjamau: Ashe karamar da tsohon shugaba Jammeh yake rabawa ta bogi ce
Kanjamau: Ashe karamar da tsohon shugaba Jammeh yake rabawa ta bogi ce

Wasu masu cutar kanjamau sun kai tsohon shugaban kasar Gambia kara, bayan da ya kulle su yayi aikin gwaje-gwajen magungunansa na cutar kanjamau da yace yana iya warkarwa, lokacin yana mulkin kasar Gambiya.

Lauyoyin peshan din da shugaban ya kwantar, su-su ukku, sunce Jammeh, ya azabtar dasu, kuma ya killace su maimakon ya barsu su karbi magani a asibitoci.

Jammeh, a lokacin da yake mulki, yace karamarsa na iya warkar da cutuka kamar su kuturta, kanjamau, tarin fuka da asthma.

DUBA WANNAN: Mutum 17m ne suka tsere daga Afirka

Lauyoyin sun shigar musu da karar ne, amma kuma shugaban ya tsere daga kasar tun watan Yanairun bara, bayan da ya fadi zabe, amma yaki barin mulki.

Najeriya ta tura sojoji domin korarsa, inda daga karshe, ya hakura ya sauka ya koma kasar Gini da zama.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel