Hoton 'yar sarkin Makkah a cikin mota ya jawo ana yamutsa gashin baki
Rahotanni sun kawo cewa wani hoton diyar sarkin Makkah Gimbiya Hayfa bint Abdullah al-Sa'ud, da aka wallafa a bangon mujallar Vogue na wannan watan ya ja hankulan mutane matuka.
A hoton dai Gimbiya Hayfa na sanye ne da fararen tufafi inda aka gano ta zaune a cikin wata haddadiyar mota a hamada.
Mujallar, ta bayyana zaman kasaitar da Gimbiyar ta yi a cikin motar da kuma yadda ta rike kambun sitiyarin motar cike da kwarewa, tana mai alakanta hakan da irin sauye-sauyen da ake kan samu a kasar ta Saudiyya.
Sai dai ba a ambato barazanar da matan da suka yi fafutukar ganin an kyale mata su tuka mota ke fuskanta ba.
An tsare wasu mutane masu mahimmanci da dama bayan da aka umarce su da kar su yi magana game da batun, duk kuwa da cewa ranar da Saudiyya ta sa don bai wa mata damar su fara tuka mota na cigaba da karatowa.
Masu fafutuka a kasar sun caccaki mujallar sakamakon rashin yin bayani akan irin lamuran da ya shafe su, da kuma bayyana Gimbiya Hayfa a matsayin wacce ta fi yin hobbasa wajen nema wa matan kasar samun 'yancin tukin mota al'amarin da bai yi wa masu rajin dadi ba.
KU KARANTA KUMA: Cin hancin 46k kacal na baiwa yan sanda suka bani motar sata – Dan jarida
Wani dan kasar ya ce abun ya yi matukar ba su takaici dangane da yadda mujallar ta Vogue Arabia ta nuna kamar gimbiyar ce kirjin biki wajen neman wannan 'yanci ba tare da nuna kokarin masu fafutukar ba.
Idan bazaku manta ba kasar Saudiyya ta sanar da cewa daga ranar 24 ga watan Yuni, matan kasar za su sami izinin fara tukin mota a cikin daular.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku bi shafukanmu domin samun labarai https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga hanyar mallakar sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng