Ba bu dan siyasar da bai sata a Najeriya - Gwamna Okorocha
Gwamnan jihar Imo dake a shiyyar kudu maso gabashin Najeriya kuma shugaban gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki Rochas Okorocha ya bayyana cewa dole ne duk wani dan siyasa a Najeriya dole ne yayi sata sannan ya rayu saboda albashin su ba wani bane.
Gwamnan wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake fira da wakilin gidan talabijin din nan mai zaman kanta ta Channels ya bayyana cewa albashin gwamna a Najeriya Naira dubu dari bakwai ne kacal kuma baya isar su.
KU KARANTA: Yadda wani malami ya fiddawa budurwa aljannu a coci
Legit.ng ta samu cewa gwamnan ya kuma kara da cewa don haka dole dukkan wani dan siyasar da baya wata kwakkwarar sana'a da yake samun kudi banda albashin sa yayi sata.
A wani labarin kuma, Jami'an hukumar nan dake yake da cin hanci da rashawa a Najeriya ta EFCC dake a garin Fatakwal, jihar Ribas sun sanar da samun nasarar cafke wani babban malamin addinin kirista mai suna Fasto James Ezekiel bisa laifin damfara.
Kamar dai yadda muka samu, Fasto James Ezekiel din ya damfari wani mutum ne da sunan wai ya samo kwangilar Naira biliyan 1.8 don haka ne ma ya bukaci mutumin da ya bashi Naira miyan 1 da dubu dari 3 domin fitar da ita.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng