Kotu ta yanke wa Nyame hukuncin daurin shekara 14 a gidan yari

Kotu ta yanke wa Nyame hukuncin daurin shekara 14 a gidan yari

Idan ba a manta ba, babbar kotu dake birnin tarayya ta samu tsohon gwamnan jihar Taraba Jolly Nyame da laifin wawushe kudin jihar wanda yawan shi ya kai kimanin naira biliyan 1.6 a lokacin da yake gwamna.

A zaman da kotun tayi a yau Laraba, 30 ga watan Mayu, Alkali Adebukola Bankole ya bayyana cewa irin yadda Nyame da makarraben sa suka yi sama da fadi akan kudaden da yadda akayi ta dibar su gunduwa gunduwa, yayi kama da labarin kasurgumin barawon nan mai suna Ali Baba da Barayin sa arba’in.

Wani da ya ba da shaida a kotun yace tun farko dai an fara satar ne da dibar miliyan 345 daga asusun gwamnati inda aka saka a asusun wani kamfani mai Saman global.

Kotu ta yanke wa Nyame hukuncin daurin shekara 14 a gidan yari
Kotu ta yanke wa Nyame hukuncin daurin shekara 14 a gidan yari

Da yake yanke hukunci, alkalin kotun yace Nyame ya amsa laifuka 21 ciki 47 da ake tuhumar sa a kai. A dalilin haka kotu ta yanke masa zaman kurkuku har na tsawon shekaru 14, babu tara.

KU KARANTA KUMA: Gwamnonin Jihohin APC za su yi yaki kan zaben Jam’iyyan da za ayi

Nyame zai garzaya gidan maza ne kai tsaye ko kuma ya daukaka kara.

Nyame yayi gwamna a jihar Taraba ne daga 1999 zuwa 2007.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel