Tirkashi: Wani Fusataccen Miji ya yiwa Matarsa da Surikarsa mummunan sara

Tirkashi: Wani Fusataccen Miji ya yiwa Matarsa da Surikarsa mummunan sara

- Yanzu haka dai wata Mata da Mahaifiyarta na can kwance a sibiti cikin mawuyacin hali

- Tun bayan da Mijinta ya kai musu hari da Adda a yankin karamar hukumar Ikpoba-Okha a Benin

- Amma sai jami'an 'Yan sanda sun samu nasarar cafke shi har ma ana shirin gurfanar da gaban shari'a

Shi dai Mijin Matar da ake zargi mai suna Iyen Igiebor an bayyana cewa yana cikin halin fushi ne sakamakon korosa da aka yi daga kasar waje inda ya tafi domin neman kudi.

Tirkashi: Wani Fusataccen Miji ya yiwa Matarsa da Surikarsa mummunan sara
Tirkashi: Wani Fusataccen Miji ya yiwa Matarsa da Surikarsa mummunan sara

Lamarin dai ya faro tun bayan dawowarsa amma ba shi da mazaunin kansa, daga bisa sai ya je gidan Surikar tasa domin ya dauki Matarsa suje wani sabon gida da ya samu. Sai dai kuma Matar tasa ta bayyana masa cewa ba ta son waccen unguwar da yake nufi.

KU KARANTA: Barayin Shanu sun salwnatar da rayuka 3 da raunata mutane 4 a jihar Kaduna

A bisa hakan ne hayaniya ta afke a tsakanin Mijin da Matarsa sannan Surikarsa ta sanya baki, daga karshe har cacar baki ta kawo rabuwarsu. Ashe hakan bai yi masa dadi ba, shi ne ya lababa yayi musu kwantan bauna yayin da suke dawowa daga kasuwa da 9pm na dare.

Jaridar Punch ta rawaito cewa fusataccen Mijin yayi niyyar fille kanta ne amma sai tayi yunkurin kare kanta ta hanyar sanya hannunta domin ta kare saran, wanda hakan yayi sandiyyar samun mummunan rauni a kafadarta.

Sannan ya kuma kaiwa Mahaifiyarta sara inda ya same ta a kanta da kuma fuskarta.

Ihun Matan ne ya janyo hankalin Makwabtan wurin da abin ya faru suka kawo musu dauki domin cetonsu, sannan kuma ‘Yan sanda suka zo suka damke shi.

Yanzu haka dai Lauyan Matar da Mahaifiyarta Mr. Jefferson Uwoghiren ya bayyanawa majiyarmu a jiya cewa sun shirya shigar da kara Kotu domin hukunta wanda ake zargin.

Yayin da su kuma Matar da Mahaifiyarta ke cigaba da karbar Magani a asibiti domin farfadowa daga wannan hali da ya jefa su ciki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel