Ramadan: Kalli yadda Sarkin Kano yake karatun Al-Qur’ani a Masallacin Annabi (SA.W)
Dayake ana cikin watan Azumin Ramadan, inda jama’a da dama ke tafiya kasar Saudiyya da nufin gudanar da aikin Umara, da nufin ibada, tare dsa fatan Allah madaukakin Sarki zai karba.
Legit.ng ta ruwaito shima Sarkin Kano, mai martaba Alhaji Muhammadu Sunusi II ba’a barsa a baya ba, inda aka hange shi a masallacin Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi dake birnin Madina, a ranar Asabar 26 ga watan Mayu.
KU KARANTA: Miyagun mutane sun afka makarantar Mata, sun yi ma 15 fyade sun jikkata da dama
Wata hadimar Sarki Sunusi, Sa’datu Baba Ahmad ce ta daura wannan hoto a shafinta na kafar sadarwar zamani na Facebook, inda tace Sarkin na karatun Al-Qur’ani mai tsarki ne a lokacin da aka dauke shi hoton.
A wani labarin kuma, a kwanakin baya ne aka kama wani karamin yaro dake amfani da sunan Mai martaba Sarki a shafin Instagram yana karbar kudade daga jama’a.
Shafin wannan yaro ta gawurta har sai da kamfanin Instagram ta bashi alamar shafin Sarki Sunusi na gaske, sau dai dubunsa ta cika ne a lokacin da ya nemiw wata yar jarida ta bashi kudi zai biya wasu mawaka da suka yi masa waka, a yanzu dai an gurfanar da yaron gaban Kotu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng