Ranar demokaradiyya: Abubuwa 5 da suka sanya jawabin shugaba Buhari na 2018 yayi shige da jawabinsa na 2016
Talata, 29 ga watan Mayu, 2018, ya kasance shekaru uku da da shugaba Muhammadu Buhari ya karbi mulki a matsayin shugaban kasa a Najeriya.
Shugaba Muhammadu Buhari yayi jawabin akan cikar demokradiyyar Najeriya shekaru 19 sannan kuma cikar gwamnatinsa shekaru uku bisa mulki.
Abubuwa biyar sun sanya jawabin shugaban kasar na 2018 yayi shige da jawabinsa na 2016, wadanda suka hada da maganar Boko Haram, yaki da rashawa, tallafin Npower, Niger Delta, da kuma ilimi, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
1. Boko Haram
Shugaba Buhari a jawabinsa na ranar dimokuradiyya a shekarar 2016 yayi jawabin akan kungiyar Boko Haram. Shugaban kasar yace ‘yan ta’addan sun kama kananan hukumomi 14, sun kuma kori jami’an tsaro daga yankunan, sannan sun tayar da tutarsu. Shugaban kasar a jawabinsa na shekarar 2018 yayi magana akan ‘yan ta’addan, inda yace gwamnatinsa ta ragewa kungiyar karfi sosai inda har tayi nasarar ceto ‘yan matan chibok 106 sai kuma ‘yan matan Dapchi 104, tare da sauran mutanen kauyuka 16,000 wadanda ‘yan kungiyar suka kama.
2. Yaki da rashawa
Shugaba Buhari a jawabinsa na 2016 yayi magana akan yaki da rashawa, inda hra ya bawa hukumar yaki da rashawa damar kama duk wani ma’aikaci data samu da laifin aikata rashawa, sannan kuma an sanar da shari’a abubuwan da mutanen Najeriya ke tsammani daga garesu akan yaki da rashawa. Shugaban kasar a jawabinsa na 2018 yace mutanen Najeriya dana kasashen waje sunyi jinjina ga kasar bisa ga kokarin da takeyi wurin yaki da rashawa.
3. Tallafin Npower
Shugaba Buhari a jwabinsa na 2016 yayi magana akan tallafin Npower wanda aka fara domin tallafawa wasu fita daga talauci, sannan kuma zai kasance hanyar dogaro da kai ga wasu da dama. Yace gwamnatinsa ta fitar da naira biliyan dari biyar a kasafin 2016, domin bangarori biyar na ayyukan cigaba. A shekarar 2018, a jawabinsa, shugaban kasar yace matasa 20,000aka zaba domin ayyukan gini (N-Build) tare da kungiyar tsara ayyukan cigaba ta kasa da kuma ungiyar magina masu rajista a kasa.
4. Niger Delta
Shugaba Buhari a jawabinsa na ranar dimokuradiyya na shekarar 2016 yace harin da ‘yan ta’adda ke kaiwa a bubutan mai na gwamnati ba zai hana gwamnatinsa sanya shuwagabannin yankin ba wurin magance matsalolin dake damun yankin. Sannan a shekarar 2018 shugaban kasar yace yankin Niger Delta ya samu ingantaccen zaman lafiya ta hanyar shiga cikin al’amuran wayewa da kuma hanyar shuwagabannin kirki na yankin da mutanen kirki. Gwamnati na kokarin kafa zaman ingantaccen lafiya, da tsaro, da kuma hanyar cigaba a yankin.
KU KARANTA KUMA: Ranar Demokaradiyya: Batutuwa 5 da Shugaba Buhari ya tabo a jawabinsa
5. Ilimi
Sannan a karshe shugaba Buhari a jawabinsa na 2016 na dimokuradiyya yace ta hanyar ilimi, gwamnatinsa zata tallafawa dalibai masu karatun kimiyya da fasaha, da fannin injiniyarin da lissafi, don gina hanyar cigaba saboda matasanmu na gobe. A jawabinsa na 2018, shugaban kasar yace fannin ilimi nata kara samun cigaba musamman kananan makarantu saboda inganta ilimin matasan Najeriya. Shugaban kasar yace a cikin shekaru uku da suka gabata gwamnatinsa ta bayar da izinin bude manyan makarantun gaba da sakandare 26 a jihohi 4 na kasar nan.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi jawabi ga ‘yan Najeriya a ranar demokaradiyya, inda ya tunawa ‘yan Najeriya cika shekaru 19 da Najeriya ta dawo turbar yanci.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng