Daya daga cikin barayin da suka fasa bankuna a Arewa ya sake fallasa wata ta'asar sa

Daya daga cikin barayin da suka fasa bankuna a Arewa ya sake fallasa wata ta'asar sa

Daya daga cikin barayin da suka fasa bankuna da dama a garin Offa, dake a jikin jihar Kwara dake zama daya daga cikin jahohin shiyyar Arewa ta tsakiya a Najeriya Michael Adiku ya sake fallasa wata katobarar da yayi.

Michael Adiku dai na zaman daya daga cikin jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya da ta kora kuma shugaban barayin da suka kai samame a bankunan a watanin baya wanda tuni ya ansa laifin sa.

Daya daga cikin barayin da suka fasa bankuna a Arewa ya sake fallasa wata ta'asar sa
Daya daga cikin barayin da suka fasa bankuna a Arewa ya sake fallasa wata ta'asar sa

KU KARANTA: Fira da Fatima, diyar Jarumi Rabi'u Rikadawa

Legit.ng ta samu cewa sai dai da yana karin haske game da yadda suka tafka satar ta bankuna, Michael ya bayyana cewa shi kadai ya kashe akalla mutane ashirin a ranar kadai ciki kuwa hadda 'yan sanda wadanda dama can ya sha alwashin sai ya rama abunda suka yi masa.

A wani labarin kuma, Wasu daga cikin 'yan ta'addan kungiyar nan ta Boko Haram har su 17 da suka mika wuya ga dakarun jami'an tsaron Najeriya a kwanakin nan sun bayyana cewa dalilin da yasa suka mika wuya shine saboda sunji ance wai shugaba Muhammadu Buhari na ce zai yi masu afuwa.

Alhasan Ahmed da ke zaman daya daga cikin 'yan ta'addan da suka mika wuya ne dai ya shaidawa kwamandan rundunar sojin Najeriya din ta Operation Lafiya Dole dake yaki da 'yan Boko Haram din a garin Maiduguri Manjo Janar Rogers Nicholas hakan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel