Ronaldinho zai auri mata biyu a wani labarin soyayya mai sanyaya rai

Ronaldinho zai auri mata biyu a wani labarin soyayya mai sanyaya rai

- Matashin dan wasan kwallon kafa Ronaldinho zai auri mata biyu a lokaci daya

- Yan matan dai suna zaune lafiya tare da Matashin a gidansa

- Rahoton ya bayyana cewa dan wasan kwallon ba bawa masoyan £1,500 don suyi rayuwar su yanda suke so

Ronaldinho zai auri mata biyu a wani labarin soyayya mai sanyaya rai
Ronaldinho zai auri mata biyu a wani labarin soyayya mai sanyaya rai

Ronaldinho dai zai auri yan mata biyu a lokaci daya.

Yan matan dai suna zaune lafiya a gidan dan wasan dake £5m Rio De Janeiro tun a watan Disamba.

Ronaldinho ya fara soyayya da Beatriz a shekarar 2016 Sannan yaci gaba da alakar sa da Priscilla wanda suke tare tuntuni.

Rahoton ya bayyana cewa masoyan suna karbar £1,500 daga wajen dan wasan don su kashe yanda suka so.

Yanayi musu kyauta iri daya a duk lokacin daya tashi kamar yanda yasai musu turare iri daya a wata tafiya da sukayi tare.

Zai auri yan matan ne a wajen wani wajen gudanar da taro dake Santa Monica Condominium inda yake zaune tun 2015.

DUBA WANNAN: A makon nan najeriya zata balle - Biafra

Wata yar uwar dan wasan mai suna Deisi tace bazata halarci bikin nasa ba.

Wani mawaki dan Brazil Jorge Versillo wanda makoci ne na Ronaldinho yace ya dauki nauyin kidan da za'a gudanar a bikin.

A watan Mayun daya gabata ne ya tura hotunan sa tare da yan matan nashi a shafinsa na Instagram.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel