Kudurin doka kan albarkatun ruwa da Buhari ya aike majalisa ya raba kawunan 'ya'yan ta

Kudurin doka kan albarkatun ruwa da Buhari ya aike majalisa ya raba kawunan 'ya'yan ta

Wani kudurin doka da ya samo asali daga bangaren zartarwa a Najeriya da shugaba Muhammadu Buhari ke jagoranta da ke da alaka da yin gyaran fuska ga dokar kula da albarkatun ruwa ya raba kawunan 'yan majalisar tarayyar kasar.

Kamar dai yadda muka samu, mafiya yawan 'yan majalisar daga arewacin Najeriya sun nuna goyon bayan su game da kudurin yayin da kuma mafiya yawan 'yan majalisun daga kudancin kasar suka nuna matukar adawar su ga kudurin.

Kudurin doka kan albarkatun ruwa da Buhari ya aike majalisa ya raba kawunan 'ya'yan ta
Kudurin doka kan albarkatun ruwa da Buhari ya aike majalisa ya raba kawunan 'ya'yan ta

KU KARANTA: Kiristoci a Ibadan sun rantse sun ga Annabi Isa cikin farin dutse

Legit.ng dai ta samu cewa kudurin dokar na da nufin baiwa gwamnatin tarayya karin iko ne game da yadda za'a rika tafiyar da harkokin gudanarwar albarkatun ruwa na kasar.

A wani labarin kuma, Gwamnatin jihar Neja dake a shiyyar Arewa ta tsakiya a ta bakin kwamishinan ta na ma'adanai Hajiya Ramatu Yar'adua ta bayyana cewa an samu rijiyoyin bakwai da aka haka a jihar da danyen mai mai tarin yawa da za'a fara fitarwa nan ba da dadewa ba.

Kwamishiniyar ta bayyana hakan ne a lokacin da ta kira wani taron manema labarai a garin Minna a ranar Alhamis din da ta gabata inda kuma ta cewa dukkan rijiyoyin an gina su ne a kwarin Bida na jihar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel