Wasu Kiristoci a garin Ibadan sun rantse cewar sun ga Annabi Isa a cikin wani dutse

Wasu Kiristoci a garin Ibadan sun rantse cewar sun ga Annabi Isa a cikin wani dutse

Bayyanar ababen dake nuna tabbatuwar imani da ababen bauta a wurare masu ban mamaki a wasu lokuttan ba sabon abu bane musamman ma a tsakanin al'ummar Najeriya mabiya addinin musulunci da kiristanci.

A wannan lokacin ma dai maganar dake ta tashe a gari itace ta wasu mabiya addinin kirista a garin Ibadan dake zaman babban birnin jihar Oyo da suka ce sun ga siffar Annabi Isa a cikin wani dutse.

Wasu Kiristoci a garin Ibadan sun rantse cewar sun ga Annabi Isa a cikin wani dutse
Wasu Kiristoci a garin Ibadan sun rantse cewar sun ga Annabi Isa a cikin wani dutse

Wasu Kiristoci a garin Ibadan sun rantse cewar sun ga Annabi Isa a cikin wani dutse
Wasu Kiristoci a garin Ibadan sun rantse cewar sun ga Annabi Isa a cikin wani dutse

KU KARANTA: Ango ya saki amaryar sa minuta 15 da yin aure

Legit.ng ta samu cewa wani ma'abocin anfani da kafar sadarwar zamani ta Facebook ne mai suna Victor Adedeji Prince ya fara watsa hotunan a shafin sa inda kuma daga nan labarin ya cigaba da yaduwa kamar wutar daji.

Wasu Kiristoci a garin Ibadan sun rantse cewar sun ga Annabi Isa a cikin wani dutse
Wasu Kiristoci a garin Ibadan sun rantse cewar sun ga Annabi Isa a cikin wani dutse

Kawo yanzu dai hotunan suna cigaba da jan hankalin al'umma da dama inda wasu ke ganin hakan abu ne mai yiwuwa yayin da kuma wasu ke ganin labarin na kanzon kurege ne kawai.

Wasu Kiristoci a garin Ibadan sun rantse cewar sun ga Annabi Isa a cikin wani dutse
Wasu Kiristoci a garin Ibadan sun rantse cewar sun ga Annabi Isa a cikin wani dutse

A wani labarin kuma, Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya watau Christian Association of Nigeria, CAN ya wanken kansa daga dukkan zargin da ake yi masa na cewa wai kungiyar ta karbi kyautar kudi daga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Shugaban kungiyar yayi wannan jawabin ne a ta bakin babban Sakataren ta na kasa Rabaran Dakta Adeniyi Adeyemi yayin da ake kaddamar da shugabannin kungiyar na jihar Ogun.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng