Abunda nake bukata daga gwamnatin tarayya a yayinda na cika shekara 60 - Falana

Abunda nake bukata daga gwamnatin tarayya a yayinda na cika shekara 60 - Falana

- Babban masanin hakkin dan adam femi Falana, yayi godiya ga shugaba Muhammadu Buhari, bisaga addu’ar da yayi masa a bikin cikarsa shekara 60 a ranar 20 ga watan Mayu

- Falana ya bayyana cewa yayi matukar farin ciki da irin kaunar da shugaba Muhammadu Buhari ya nuna masa a ranar bikin cikarsa shekara 60

- Falana ya bukaci gwamnatin tarayya da ta saki wadannan ke tsare ba bisa ka’ida ba a fadin kasar a matsayin kyautar da gwamnatin tarayyar zatayi masa

A ranar 24 ga watan Mayu, a jihar Legas, NAN ta ruwaito cewa Babban masanin hakkin dan adam femi Falana, yayi godiya ga shugaba Muhammadu Buhari, bisa ga addu’ar da yayi masa a bikin cikarsa shekara 60 a ranar 20 ga watan Mayu.

Falana ya bayyana godiyar tasa ne a wani sako da ya aikawa jaridar News Agency Nigeria (NAN) a jihar Legas.

Falana ya bayyana cewa yayi matukar farin ciki da irin kaunar da shugaba Muhammadu Buhari ya nuna masa a ranar bikin cikarsa shekara 60.

Falana ya bukaci gwamnatin tarayya da ta saki wadannan ke tsare ba bisa ka’ida ba a fadin kasar a matsayin kyautar da gwamnatin tarayyar zatayi masa.

Abunda nake bukata daga gwamnatin tarayya a yayinda na cika shekara 60 - Falana
Abunda nake bukata daga gwamnatin tarayya a yayinda na cika shekara 60 - Falana

NAN ta ruwaito cewa shugaba Buhari a ranar Asabar ta bakin mai bawa shugaban kasar shawara ta fannin sadarwa Femi Adesina, yayi jinjina ga kokarin da Falana yayi na kishin kasa na tsawon shekaru.

KU KARANTA KUMA: Labari mai dadi: Shugabar ma’aikata ta tarayya na kokarin kara albashin ma’aikata don inganta ayyukan gwamnati

Shugaban kasar ya kuma roki ubangiji ya kara masa tsawancin kwana da lafiya da kuma imani da zai cigaba da kishin kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng