Tashin hankali ba’a sa miki rana: Wata Giwa ta mitsitstsike wani manomi har lahira a gonarsa

Tashin hankali ba’a sa miki rana: Wata Giwa ta mitsitstsike wani manomi har lahira a gonarsa

Wani matashin manomi mai shekaru 35, Zuberi Maocha ya gamu da ajalinsa a hannun wata Giwa da ta balle ta fita neman abinci a Gundumar Tunduru dake yankin kudancin Tanzaniya, inji rahoton kamfanin dillancin labaru.

Mutuwarsa ta auku ne a ranar Laraba, 23 ga watan Mayu, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban kkauyen Mishaje, Wema Waziri ya tabbatar, inda yace Zuberi ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da ya yi namijin kokarin fatattakar wasu Giwaye da suka shigar masa gona.

KU KARANTA: Buhari ya yi gaskiyar, Obasanjo ne silar tabarbarewa wuta a Najeriya – Atiku Abubakar

Waziri ya kara da cewa gonar Zuberi na nan ne gab da gandun dabbobi na Selous, daya daga cikin manyan gandun dabbobi a Duniya dake dauke da Giwaye sama da dubu ashirin.

“Da misalin karfe 1 na ranar Talata 22 ga watan Mayu ne wasu Giwaye suka fada gonar Zuberi, inda shi kuma ya yi kokarin fatattakarsu don kada su yi masa barna, sai dai yana cikin kokarsu ne sai wata Giwa dake shayarwa ta yi kansa, inda ta tattake shi har sai ya mutu.” Inji shi.

Shi ma wani ma’aikaci da hukumar kula da namun daji na Chingoli, Nombo Sandari ya bayyana cewa kafin mutuwar manomin, ya yi ta ihun neman agaji, amma babu wanda ya kai masa.

Da yake tabbatar da lamarin, jami’in kula da namun daji na Tunduru, Limbega Ally yace tuni suka aika da masu kula da namun daji su 11 da nufin maido da Giwayen gandunsu, don gudun kada su sake hallaka mutane.

Bincike ya nuna adadin Giwaye dake kasar Tanzani sun ragu daga dubu dari da tara, 109,000 a shekarar 2009 zuwa dubu arbain da uku, 43,000, a shekarar 2015.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel