'Yan ta'adda 700 na Boko Haram sun shirya saduda - Gwamnatin Najeriya
A yayin da ta'addanci a yankin Arewa masao Gabashin Najeriya ya ki ci ya ki cinyewa tun kimanin shekaru 9 da suka gabata, gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa akwai kimanin mayaka 700 ne Boko Haram suka bayyana ra'ayin su na mika wuya da saduda a halin yanzu.
Babban Jakadan Najeriya a majalisar dinkin duniya, Tijjani Bande, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da reshen tsaro na majalisar.
Mista Bande ya bayyana cewa, akwai kimanin mutane miliyan 14.8 da rikicin boko haram ya shafa yayin da mutane miliyan 1.7 suke gudun hijira wanda mafi akasarin su mata ne da kuma kananan yara.
Kamar yadda shafin jaridar Premium Times ya bayyana, Mista Bande ya yi wannan fashin baki ne yayin halartar muhawara akan bayar da kariya ga sauraran al'umma yayin da dakarun soji ke tunkarar tarzoma.
KARANTA KUMA: Madallah: Gwamnatin Tarayya ta bayyana adadin Kudade na rarar Ma'aikatan Bogi
Jakadan ya bayar da tabbacin cewa, tsare-tsare na gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na matukar tasiri kwarai da aniyya wajen kawo tallafi da kuma agaji ga yankin Arewa maso gabashin Najeriya da a halin yanzu ya daidaita a sanadiyar ta'addanci.
Ya kara da cewa, akwai shirye-shirye gami da tsari masu tasirin gaske da gwamnatin shugaba Buhari ta gindaya domin bayar da kariya ga al'umma musamman mata da kananan yara a yankin na Arewa maso Gabas.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng