Na dawo da karfi na kuma zan kuma cigaba da gwagwarmaya - Melaye

Na dawo da karfi na kuma zan kuma cigaba da gwagwarmaya - Melaye

- Dino Melaye ya saki zafafen kalamai tare da gugar zana hadi da jirwaye mai kama da wanka

- Maganganunsa na dauke da yabo ga Mutanensa mazabarsa da kuma 'yan uwansa 'yan Majalisa

- Ya fadi haka ne yayinda 'Yan sanda ke cigaba da tsare shi

Sanatan Kogi ta yamma Sanata Dino Melaye ya godewa ‘yan Najeriya bisa yadda suka nuna masa goyon bayan a ‘yan satittikan da suka gabata, yace ya so yin magana amma da yaga yadda Mutane suka shiga cikin lamarin yaki da bita da kulli da siyasar bata suna da ake masa, sai ya ja bakinsa.

Sakon godiya ga ‘Yan Najeriya na dawo da karfi na kuma zan cigaba da fadar gaskiya - Melaye
Sakon godiya ga ‘Yan Najeriya na dawo da karfi na kuma zan cigaba da fadar gaskiya - Melaye

“sun bude min duk wata kofar matsi, ta hanyar tauye min duk wata dama da nake da ita, amma da taimakon Mai duka da kuma goyon bayanku ‘yan Najeriya gaskiya ta dankara karya da kasa.”

“wani mai hikima yana cewa, idan masu mugun nufi suka fara tarayya to ya zama dole masu gaskiya su hada kansu ko kuma a rinka yi musu dauki dai-dai”

Wadannan wasu daga cikin kalaman Sanatan ne a lokacin da ya aikewa da wakilin jaridar Daily Trust sako ta kafar sadarwa ta Whatsapp.

KU KARANTA: Atiku ya karyata cewar ya ziyarci tsohon gwamnan jihar Filato a gidan yari

A cikin sakon Sanatan ya mika godiyarsa ga Mutanan Jiharsa ta Kogi bisa kasancewa tare da shi da suke yi a kowanne lokaci.

Sakon godiya ga ‘Yan Najeriya na dawo da karfi na kuma zan cigaba da fadar gaskiya - Melaye
Sakon godiya ga ‘Yan Najeriya na dawo da karfi na kuma zan cigaba da fadar gaskiya - Melaye

"Da yake magana kan batun kiranyen da aka shirya masa kwanan baya cewa yayi, maimakon gwuiwarsa tayi sanyi kullum kara karfi take kasancewar Mutanensa na tare da shi a koda yaushe.

Melaye ya cigaba da mika sakon godiyarsa ga shugaban Majalisar Dattijai Sanata (Dr.) Abubakar Bukola Saraki, kasacewar ya tsaya tsayin daka wajen kare Dimukuradiyya ta hakika.

Sannan ya godewa shugaban Majalisar Wakilai Rt. Hon. Yakubu Dogara, bisa dagewa da sukai wajen ganin anbi yadda tsarin mulki ya ce, aduk fadin kasar nan.

K ya mika karin wata godiya ga ‘yan uwansa ‘yan Majalisa musamman na Dattijai bisa bin gaskiya ba, wannan shi ne yake nuni da cewa har yanzu da alamun Najeriya zata sa rai da samun shugabanni jajirtattu. A cewar Sanatan.

Daga karshe Dino Melaye ya kara jaddada matsayinsa inda ya ce, “ Zai cigaba da gwagwarmaya ba kama kafar yaro kamr yadda ya saba ba tare da ya ja birki ballantana ya tsaya ba, har sai gaskiya ta yi halinta mutukar yana raye.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel