Wata mata mai shekaru 39 a duniya ta burmawa babban malamin addini fasassar kwalba

Wata mata mai shekaru 39 a duniya ta burmawa babban malamin addini fasassar kwalba

Wata mata mai shekaru 39 a duniya kuma mai suna Esther Olawole dake a jihar Osun ta shiyyar kudu maso yammacin kasar ta gurfana a gaban kuliya bisa zargin da ake yi mata na burmawa wani babban malamin addinin kirista fasassar kwalba.

Dan sanda mai gabatar da kara dai mai suna Isifekta Emmanuel Abdullahi tun farko ya shaidawa kotun cewa wadda ake zargin ta aikata laifin ne a ranar 6 ga watan Mayu shekarar 2018 da misalin karfe 6 na yamma.

Wata mata mai shekaru 39 a duniya ta burmawa babban malamin addini fasassar kwalba
Wata mata mai shekaru 39 a duniya ta burmawa babban malamin addini fasassar kwalba

KU KARANTA: An ga watan Ramadana a jahohi da dama

Legit.ng ta samu cewa sai dai alkalin kotun Ishola Omisade ya bayar da ita beli kan kudi Naira dubu 200 sannan kuma ya dage karar har zuwa ranar 18 ga watan Yuni.

A wani labarin kuma, Jami'an rundunar hukumar hana fasa kwauri ta tarayyar Najeriya dake a shiyyar dake kula da yanki na A karkashin shugabancin Mohammed Uba a ranar Laraba ta sanar da samun nasarar cafke motocin alfarma akalla 30 da kudin su ya kai darajar Naira biliyan 1.

Kamar dai yadda rundunar ta bayyana, an kama motocin ne lokacin da ake kokarin shigowa da su ta kan iyakar Najeriya da kasashen jamhuriyar Kamaru da Benin a jahohin Legas da Ogun dukkan su a shiyyar kudu maso yammacin kasar nan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel