Kungiyoyin kamfen na Buhari da Bagudu sunyi rikici a jihar Kebbi
- Kungiyoyin kamfen na magoya bayan shugaba Buhari ya sake tsayawa takara da Gwamna Abubakar Atiku bagudu na jihar Kebbi sunyi arangama a jihar
- Kungiyoyin sune na hudu ga hudu a karkashin jagorancin Alhaji Kabiru Giant da Buhari Bagudu support organisation (BBSO) a karkashin jagorancin mataimakin gwamnan, Alhaji Faruk Enabo
- Rikicin ya fara ne sakamakon yarjejeniyar da akayi akan cewa duk wata da take ikirarin goyon bayan sake zabar shugaba Buhari su watsar da ayyukan da suke gudanarwa su dawo a hade wuri guda karkashin jagorancin Bagudu don samun tallafi
Kungiyoyin kamfen na magoya bayan shugaba Buhari ya sake tsayawa takara da Gwamna Abubakar Atiku bagudu na jihar Kebbi sunyi arangama a jihar.
Kungiyoyin sune na hudu ga hudu a karkashin jagorancin Alhaji Kabiru Giant da Buhari Bagudu support organisation (BBSO) a karkashin jagorancin mataimakin gwamnan, Alhaji Faruk Enabo.
Rikicin ya fara ne sakamakon yarjejeniyar da akayi akan cewa duk wata da take ikirarin goyon bayan sake zabar shugaba Buhari su watsar da ayyukan da suke gudanarwa su dawo a hade wuri guda karkashin jagorancin Bagudu don samun tallafi da kulawa na kirki, wanda hakan ne abokan adawar suka ki amince.
KU KARANTA KUMA: Zamu rarrabawa ‘yan Najeriya kudaden da Abacha ya sata – Shugaba Buhari
Kungiyar ta hudu ga hudu (4+4) suna daukar kungiyar BBSO a matsayin ‘yan yaudara, su kuma BBSO suna kallon sauran kungiyoyin a matsayin na bogi wadanda baza’a iya yadda dasu ba, kuma hakan ya kawo rarrabuwar kawunan a tsakanin ‘yan jam’iyyar ta APC.
A halin da ake ciki, yan siyasa ya cigaba da baje gwanjinsu a daidai wannan lokaci da guguwar zaben 2019 ke gabatowa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng