Zan karbi shawarar sauke ni da farin ciki – Kakakin majalisar jihar Kano

Zan karbi shawarar sauke ni da farin ciki – Kakakin majalisar jihar Kano

- Shugaban majalisar jihar Kano, Alhaji Yusuf Abdullahi Ata yace a matsayinsa na musulmi wanda ya yadda da kaddara mai kyau da mara kyau, zai karbi hukuncin sauke shi a matsayin kaddara mai kyau

- Ata yace yunkurin da wasu cikin ‘yan majalisar keyi na saukeshi bashi da wata alaka da rashin cancanta

- Yace a kowane abu akwai farkonshi sannan kuma yana da karshe, kamar yadda idan Allah yace lokacin saukata yayi ba wanda zai iya hanani sauka haka zalika idan kuma lokacin saukata baiyi ba babu wanda ya isa ya saukeni

Kakakin majalisar jihar Kano, Alhaji Yusuf Abdullahi Ata, yace a matsayinsa na musulmi wanda yayi imani da kaddara mai kyau da mara kyau, zai karbi hukuncin sauke shi a matsayin kaddara mai kyau.

Ata ya bayyanwa manema labarai cewa yunkurin da wasu cikin ‘yan majalisar keyi na saukeshi bashi da wata alaka da rashin cancanta.

Yace a kowane abu akwai farkonshi sannan kuma yana da karshe, kamar yadda “idan Allah yace lokacin saukata yayi ba wanda zai iya hanani sauka haka zalika idan kuma lokacin saukata baiyi ba babu wanda ya isa ya saukeni.

Zan karbi shawarar sauke ni da farin ciki – Kakakin majalisar jihar Kano
Zan karbi shawarar sauke ni da farin ciki – Kakakin majalisar jihar Kano

“Farin cikina shine ban saci kudin kowa ba. Saboda haka, idan yau aka sauke ni daga kujerar shugaban majalisa zan bari kuma babu wanda zai zargeni da satar kudin mutane. Ina da mazabar da nake wakilta saboda haka bazan iya yiwa mazaba ta aiki ba sannan kuma nayiwa mazabobin sauran ‘yan majalisa ba a lokaci daya.”

KU KARANTA KUMA: Ramdan: Kungiyar JIBWIS reshen jihar Katsina ta rabawa malamai kayayyakin Azumi

A baya Legit.ng ta rahoto cewa an tura yan sandan su kulle majalisar ne tun karfe 2 na dare domin hana yan majalisan dokokin shiga.

Masu sharhi sun bayyana cewa wannan abu ba zai rasa alaka da shirin tsige kakakin majalisar dokokin Kano, Alhaji Yusuf Abdullahi Ata, da wasu shugabannin majalisan ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel