Kun ga budurwa mai shekaru 25 daga Arewa da ta kammala digirin digir-gir din ta

Kun ga budurwa mai shekaru 25 daga Arewa da ta kammala digirin digir-gir din ta

Kamar yadda muka samu, wani abun alfahari ya samu al'ummar arewacin Najeriya bayan da aka samu wata budurwa mai kananan shekarun da ba za su wuce 25 ba a duniya da ta kammala digirin digir-gir a jami'ar Covenant mai suna Chiamaka Deborah Motilewa.

A cikin yanayi mai cike da sha'awa da murna ne dai budurwar ta sanar da hakan a shafin ta na dandalin sadar da zumunta na Tuwita inda ta bayyana cewa ta samu kammala karatun na ta ne a bangaren harkokin kasuwanci.

Kun ga budurwa mai shekaru 25 daga Arewa da ta kammala digirin digir-gir din ta
Kun ga budurwa mai shekaru 25 daga Arewa da ta kammala digirin digir-gir din ta

KU KARANTA: Wata Hajiya mai safarar muggan kwayoyi tayi batan dabo a Arewa

Legit.ng dai ta samu haka zalika cewa Dakta Chiamaka Deborah Motilewa yar asalin jihar Kogi ce dake a Arewacin Najeriya ta tsakiya sannan kuma an haife ta kuma girma a garin Jos.

Daman dai ko shakka babu yankin na arewacin Najeriya Allah ya albarkace su da hazikan mutane masu dumbin basira da hazaka a dukkan fannoni na rayuwa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel