Idan ajali yayi kira: Wata Damisa ta cinye wani yaro dan shekara 3

Idan ajali yayi kira: Wata Damisa ta cinye wani yaro dan shekara 3

- Jami'an da ke kula da namun daji a Uganda na farautar wata damisa da ta kwace wani karamin yaro mai shekaru uku kuma ta cinye shi a daren ranar Juma'a.

- Yaron dai da ne ga daya daga cikin ma'aikata da ke aiki a wurin kula da namun daji na Queen Elizabeth National Park da ke kasar Uganda.

Idan ajali yayi kira: Wata Damisa ta cinye wani yaro dan shekara 3
Idan ajali yayi kira: Wata Damisa ta cinye wani yaro dan shekara 3

Jami'an da ke kula da namun daji a Uganda na farautar wata damisa da ta kwace wani karamin yaro mai shekaru uku kuma ta cinye shi a daren ranar Juma'a.

Yaron dai da ne ga daya daga cikin ma'aikata da ke aiki a wurin kula da namun daji na Queen Elizabeth National Park da ke kasar Uganda.

DUBA WANNAN: Duba kaga inda mata suke neman maza ruwa a jallo

Elisha Nabugyere ya bi mai renonsa waje a bangaren rukunin gidajen ma'aikata da ba a katange ba lokacin da damisar ta far masa, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

"Mai renon nasa ba ta san cewa yaron na binta a baya ba. Ta ji lokacin da ya yi ihu amma duk da cewa ta yi kokarin ceto shi daga hannun damisar amma hakarta bata cimma ruwa ba.

Damisar ta wuce da shi cikin daji, kuma an tura da wasu cikin daji domin kubutar da yaron amma sai washegari suka gano kwarangwal din kansa," a cewar kakakin hukumar kula da namun daji ta Uganda Bashiir Hangi.

"Ana kan farautar damisar domin a cafketa kuma a cireta daga sauran namun daji saboda muddin ta fara cin naman bil'dama, to za ta iya sake neman wani mutumin da za ta hallaka, a don haka tana da hadari sosai" in ji shi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel