Dandalin Kannywood: Ado Gwanja ya bayyana alakar sa da Adam A. Zango

Dandalin Kannywood: Ado Gwanja ya bayyana alakar sa da Adam A. Zango

Daya daga cikin fitattun 'yan wasan barkwanci kuma fitattun mawaka a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood watau Ado Gwanja ya fito ya karyata rade-radin da ke yawo a bakunan jama'a dangane da tabarbarewar dangantaka a tsakanin sa da takwaran sa Adam A. Zango.

Dandalin Kannywood: Ado Gwanja ya bayyana alakar sa da Adam A. Zango
Dandalin Kannywood: Ado Gwanja ya bayyana alakar sa da Adam A. Zango

KU KARANTA: An gano masu rura wutar rikicin tsakanin Adam Zango da Ali Nuhu

A wata tattaunawa da yayi da wakilin majiyar mu, Ado Gwanja ya fadi cewa duk wadannan batutuwan karya ne tsagwaron ta da makiya ke yadawa.

Legit.ng ta samu cewa haka zalika Ado Gwanja din ya kara da cewa shi suna nan tare da Adam A. Zango din lafiya kalau.

"Kasan ba a rasa wadanda basu rasa abin cewa a kullum. Su bi wurare suna yada maganganu iri-iri. Amma ni dai a nawa sanin babu abin da ya shiga tsakani na da Adam Zango.

"Hasali ma shi maigida na ne domin ni a yaron sa ne kuma a hannun sa na fara sana’a ta kuma har yan zu ma haka ne.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng