Kasar Canada na son rage yawan 'yan Najeriya da ke tururuwa zuwa kasarta

Kasar Canada na son rage yawan 'yan Najeriya da ke tururuwa zuwa kasarta

- 'Yan Najeriya na yawan guduwa kasashe masu arziki domin rayuwa

- A yanzu kasar Kanada ke kwasar jama'a daga Indiya, Larai da Afirka

- Kasar tana so ta rage yawan 'yan Najeriya masu tururuwa zuwa kasar ta

Kasar Canada na son rage yawan 'yan Najeriya da ke tururuwa zuwa kasarta
Kasar Canada na son rage yawan 'yan Najeriya da ke tururuwa zuwa kasarta

Ofishin jakadancin kasar Kanada dake nan Abuja, ya mika korafinsa ga hukumoomi a Najeriya, dama hadin kan takwarorinsa na Amurka, kan yadda 'yan kasar nan na Najeriya ke tururuwa zuwa cikin kasarsa babu kakkautawa.

A bincikensu, sun gano cewa, matasa a Najeriya, na karbar bisar Amurka da niyyar ziyara kawai domin shakatawa, amma sai su wullar da paspon nasu da sun isa Amurka, su je iyakar kasar ta Canada, su fada cikin kasar ba bisa ka'ida ba, kuma suyi zamansu su ki dawowa.

DUBA WANNAN: Abubuwa dake kashe aure a zamanin nan

A kokarin 'yan Najeriya dai, na guje wa bakin talauci na kasarsu, sukan tsere kasashen waje, inda sukan ada mugun hannu, ko a bautar dasu, ko sahara ko teku su hadiye su, ko kuma su isa amma a dawo dasu.

A bayan hawan shugaban Amurka, sai suka daina zuwa Amurkar da niyyar zaman gudun hijira, saboda rantsuwar sabon shugaba Trump na koro masu zuwa ba bisa ka'ida ba, ina suka koma bibiyar kasashe masu makwabtaka da Amurkar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel