Kuliya manta sabo: Kotu ta iza keyar wani saurayi gidan kaso sakamakon satar Kifi

Kuliya manta sabo: Kotu ta iza keyar wani saurayi gidan kaso sakamakon satar Kifi

- Wani matashi ya ga takansa a gaban wata al'kaliya

- Duk da rokon lauyan da yake kare shi, yau saurayin sai yayi kwanan gidan kaso

Yanzu haka dai wani matashi mai shekaru 23 ya tsinci kansa a gidan maza, dalilin satar kifin da yayi a unguwar Osogbo ta jihar Osun.

Yawan adadin kifin da ake zargin matashin mai suna Abiodun Olasunkanmi, da sibarewa ya kai har na N800,000.

Kuliya manta sabo: Kotu ta iza keyar wani saurayi gidan kaso sakamakon
Kuliya manta sabo: Kotu ta iza keyar wani saurayi gidan kaso sakamakon

A ranar Litinin da ta gabata ne, Dan-sanda mai gabatar da kara Abiodun Fagboyinbo, ya shaidawa kotun mai shari’a Mrs. O. A. Oloyade, cewa, wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 15 ga watan Afrilun da ya gabata da misalign karfe 5:30 na asuba.

A cewarsa, laifin ya saba da sashi na 390 (9) da kuma sashi na 34 kundi na biyu na manyan laifuka (2013) na jihar ta Osun.

Matashin dai da ake zargi, ya ki amsa laifinsa sannan ya zabi a gudanar masa da shari’a a gaggau ce. Kuma lauyan wanda ake karar Mr. Okobe Najite, ya roki kotun da ta taimaka da bayar da shi beli ba tare da tsauraran sharudda ba.

KU KARANTA: Murna baki har kunne: Amurka zata maidowa Najeriya $500m da aka sata

Daga nan ne mai shari’ar ta amince bayar da shi beli bisa sharadin kawo wandanda zasu tsaya masa akan kudi Naira N500,000, kuma dole su zama suna da takar dar shaidar biyan haraji, su kawo hotan fasfonsu sannan su kuma su rantse

Kuliya manta sabo: Kotu ta iza keyar wani saurayi gidan kaso sakamakon satar Kifi
Kuliya manta sabo: Kotu ta iza keyar wani saurayi gidan kaso sakamakon satar Kifi
Asali: UGC

Sannan mai shari’ar ta daga karar zuwa ranar 21 ga watan Mayu, amma bisa dalilin gaza cikawar sharuddan belin har ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoto ya sanya dole aka hankada matashin gidan yarin Ilesa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku

ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel