"Dawowar Sanata Ali Modu Sheriff APC ba alheri bane"
Yunkurin dawowar Sanata Ali Modu Sheriff zuwa jam'iyyar APC alheri ba be ga 'ya'yan jam'iyyar da ma 'yan Najeriya musamman 'yan jihar Borno kamar dai yadda wani tsohon dan majalisar wakilai Dakta Haruna Yerima ya bayyana.
Dakta Haruma Yerima ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilin majiyar mu inda kuma ya alakanta dawowar ta sa da wasu wadanda ba su son jam'iyyar ta su ta APC ko kadan.
KU KARANTA: Atiku ya fadi abunda zai yi a wata 6 na farkon wa'adin sa
A wani labarin kuma, Shugaban jam'iyyar APC mai mulki a jihar Borno dake a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya mai suna Ali Dolori ya bayyana matsayar sa game da labarin komawar Sanata Ali Modu Sheriff jam'iyyar APC.
Ali Dolori da alama dai ya bayyana rashin gamsuwar sa da dawowar fitaccen dan siyasar a jihar inda kuma ya zargi cewar ya dawo ne kawai domin ya kawo hargizi a zabukan shugabannin jam'iyyar da za'a gudanar.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng