Aikin assha: Wata Mahaifiya tayi bidiyon ‘ya’yanta masu shekaru 3 suna luwadi

Aikin assha: Wata Mahaifiya tayi bidiyon ‘ya’yanta masu shekaru 3 suna luwadi

- Bayan daukar yaran ne sai ta tuwara Mahaifin yaran bidiyon

- Bidiyon dai na yaran ya shahara a intanet

Kwamishinan yan sanda na jihar Lagos Edgal Imohimi, yayi holar iyayen yaran ga manema labarai tare da tabbatar da cewa irin wannan mummunar dabi’ar bata da mazauni a jihar.

Aikin assha: Wata Mahaifiya tayi bidiyon ‘ya’yanta masu shekaru 3 suna luwadi
Aikin assha: Wata Mahaifiya tayi bidiyon ‘ya’yanta masu shekaru 3 suna luwadi

Amma sai dai mahaifiyar yan biyun ta ce "laifin babansu ne, domin aurensu ya mutu tun bayan shekara guda da ta gaba ta, kuma hukumar kula da hakkin dan Adam ta sahale min yaran suna zama a wuri na, yayinda zasu na zama a wurin mahaifin nasu na tsawon awanni 12 duk karshen sati, sai dai kuma mahaifin nasu baya bin waccan dokar."

KU KARANTA: Rikicin Benuwe: Mukaddashin Gwamna yace an tasa su gaba dare da rana

wani lokacin sai sunyi kwanki da yawa kafin ya dawo da su, kuma duk lokacin da ya kawo su "ina ganin wasu sababbin dabi’u daga wujensu, ko suce min suna jin zafi a duburarsu. Na shiga cikin damuwa matuka don ban san ina yake kai su ba, amma dai naji ance baban nasu yana zaune ne da wata tsohuwa."

Wasu lokutan in suka dawo sai ta ga jini yana tsattsafowa daga duburarsu, har akwai wata rana da Malamar Makarantarsu ta kira ta a waya ta fada mata, sai ta ce mata, "Ta kira babansu domin ranar daga gidansa suka tafi makarantar."

"Ban san wanene ya koya musu wannan abin ba, amma kam tabbas cin zarafi ne, kuma a inda yake kai su ne suka koyo, ga shi kuma yanzu yana son ya dora min laifi." A cewar Mahaifiyar yaran Patience Isua.

A bangaren Mahaifin yaran kuwa mai suna Ikanta, ya musanta zargin da uwar yayan nasu tayi masa, ya ce, bata taba yi masa Magana ko nuna masa wani abu ba sai a ranar da ta tura masa da bidiyon.

ya ce, “Nayi mamakin ganin bidiyon, don ban yarda hakan zata iya faruwa ba. Amma maimakon ta hana su a lokacin, wai sai ta dauki waya ta yi bidiyonsu.”

Kwamishin yan sandan ya tabbatar da cewa, wannan babban laifi ne da baza su dauke shi da wasa ba.

Akwai hukumomin da suke kula da hakin yara da abubuwa irin wadannan kamar Ma’aikatar Matasa da cigaban al’umma, kuma duba da irin abinda da ya faru ga yaran nan, zamu iya cewa ba su samu cikakkiyar kulawar iyaye ba.

A don haka zasu mika yaran ga hukamar kula da hakkin kananan yara domin ba su kulawa ta musamman, daga nan kuma sai su duba cancanta maido musu da yaran. A cewar kwamishina Imohimi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel