Batun Farfesa mai fesar da maki ga 'yanmata masu bada hadin kai: Budurwar tayo sabon sako itama
- Monica Osagie tace ta shirya fuskantar duk wani kalubale dangane da kin amsa gayyatar da akayi mata
- Monica Osagie wadda ta yadda ta bada kanta domin Karin maki tace ta yadda da fuskanci ko wani kalubale akan halartar gayyatar da akayi mata
- Ta nemi makarantar da ta bada shaida kafin ta bayyana a gaban su. Osagie tace a shirye take data bayyana a gaban su aduk lokacin da aka bukaci hakan
Miss Monica Osagie dalibar data ki amincewa ta bada kanta matukar zata sami makin data rasa a makarantar Obafemi Awolowo Ele-Ife ta karyata gayyatar ta da hukumar makarantar tayi biyo bayan sautin murya na hirar ta da Farfesa Richard Akindele da aka samu wanda ya ke naman amincewarta.
Osagie ta karyata hakan ne ta hanyar wakilin ta Abiola Akiyode Afolabi.
Akiyode yace hukumar makarantar bata da damar da zata gayyaci Osagie zuwa gabanta.
Ta nemi hukumar makarantar ta bada wata sheda kafin ta bayyana a gabanta.
Ga abinda tace "kafin yaduwar wannan al'amari hukumar makarantar ta samu labari amma batayi komai akaiba, da ace maganar bata yaduba babu abinda hukumar zatayi..
"Ina tunanin wannan shiyafi kamata mu maida hankali akai shin dama wannan dabi'ace ta wannan professor ko kuwa dabi'ace data sabawa dokar makarantar ko kuma ya sabawa lakcarorin makarantkamataTa kara da cewa Osagie a shirye take data bayyana a gaban hukumar matukar sukayi mata gayyatar da ta kamata."
DUBA WANNAN: An kasa maganin zazzabi a Najeriya
Hukumar makarantar tayi abinda ya kamata tayi ta hanyar turo mata gayyatar data kamata, hukumar ta nada duk wani record dinta tunda dai daliba ce a makarantar, har yanzu basu gayyace ta ba amma ko yau suka nemeta zata je.
Ta kara da cewa Osagie tayi wannan rikodin dinne domin ya zama shaida "ba ta watsa wannan rikodin din ba ta ajjiye shine daga baya ta turawa wasu mutum biyu a lokacin da take neman taimako yayinda daya daga cikinsu ya watsa shi.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng