Wuya makarantar kare: Ba zan sake gwajin nukiliya ba har abada - Kim Jong-un
Labaran da muke samu da dumin su na nuni ne da cewa shugaban kasar Koriya ta Arewa watau Kim Jong-un ya bayar da sanarwar dakatar da gwajin harba makaman nukiliyar kasar sa tare kuma da rufe dukkan tashoshin da ake gwajin makaman a kasar sa.
KU KARANTA: An gano alakar Buhari da babban bishof din Ingila
Wannan matakin da ya dauka dai na zuwa ne kimanin mako daya kafin ganawar da shi Mista Kim Jong-un din zai yi da takwaran sa shugaban kasar Koriya ta Kudu Moon Jae-in mai makwaftaka da shi.
Legit.ng dai ta samu cewa Shugaba Kim Jong-un ya kuma shaida wa kwamitin zartarwa na jam'iyyar sa ta Worker's Party wasu batutuwa kusan guda shida ciki hadda cewa babu wani muhimmanci a ci gaba da gwajin makaman nukiliya.
A baya dai Mista Kim Jong-un ya sha jan zare da shugabannin kasashen Koriya ta Kudu da ma Amurka musamman ma dalilin gwajin makami mai linzamin da kasar sa ke cigaba da yi akai-akai.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng