Majalisar dattijai ta aikewa shugabannin hukumomin tsaro guda biyu sammaci a kan sace sandar majalisa
Majalisar dattijai ta aikewa shugaban hukumar 'yan sanda na kasa, Ibrahim Idris, da takwaransa na hukumar jam'iar tsarta farin kaya (DSS), Lawal Daura, sammaci.
Da yake bayyana dalilin gayyatar shugabannin hukumomin tsaron biyu, mukaddashin shugaban majalisar, Ike Ekweremadu, ya ce suna son su sanar da majalisar matsayin binciken da suka gudanar dangane da batun kutse cikin zauren majalisar tare da dauke sandar iko a yayin da majalisar ke tsaka da zama.
A jiya, Laraba, ne wasu matasa ne guda biyar suka kutsa cikin majalisar a dai-dai lokacin da Sanata Theodore Orji ke jawabi, suka dauki sandar ikon majalisar suka ruga da gudu.
Ana zargin wani Sanata, Omo Agege, da yiwa matasan jagora zuwa cikin zauren majalisar, zargin da Sanatan ya musanta.
DUBA WANNAN: Dalilin ganawa ta da Osinbajo bayan tashin hankali a majalisar dattijai
Hukumar 'yan sanda tayi nasarar cafke matasan tare da bayyana sunayen su.
Kazalika hukumar 'yan sandan ta mayar da sandan ikon majalisar ga mukaddashin mataimakin shugaban majalisar, Ike Ekweremadu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng