Mutuwar kasko: Wani jarumin kare ya mutu bayan kashe micijin da zai cutar da maigidansa (Hoto)

Mutuwar kasko: Wani jarumin kare ya mutu bayan kashe micijin da zai cutar da maigidansa (Hoto)

- Mallakar dabba domin tsaro yayi wa wani mutum rana

- Kare na daya daga cikin dabbobin dake sadaukar da rayukansu ga iyayen gidansu

Wannan hoton wani jarumin Kare ne da su kayi artabu da Micijin da yazo shiga makwancin Maigidansa.

Karen dai yayi ta haushi amma Micijin bai saurara ba, bayan fada ya kaure tsakaninsu ne Micijin na saransa shi kuma yana cizo da yakushinsa, a karshe har yayi nasarar kashe Micijin, amma sai dai kash Karen shima ya mutu sakamakon saran da micijin yayi masa.

Amma murmushin da yake fuskar Karen na bayyana cewa ya yabawa kansa da kansa domin rayuwarsa ta zama fansa ga Maigidansa.

Hoton wani jarumin kare da ya kashe micijin da zai cutar da maigidansa
Hoton jarumin Kare

KU KARANTA: Yadda akayi ‘yan ta’adda 5 suka tsallakewa jami’an tsaro 250 na majalissa kafin suka sace sandar iko

Tarihi ya nuna cewa Kare yana da kyakkyawar alaka da mutane, yakan tsare lafiyar iyayen gidansa, da iyalansu da kuma duk wani abun da suka mallakarsu.

wani lokacin ma har aikensa ake da sako ya kai ta hanyar rataya masa a wuya.

Fulani ma kanyi amfani da shi wajen taya su kiwon dabbobinsu musamman ida suna da yawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku

ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng