Wata kungiyar musulmi, na so a sake canja fasalin Naira dari, ji dalilinsu

Wata kungiyar musulmi, na so a sake canja fasalin Naira dari, ji dalilinsu

- Kungiyar musulmai sun bukaci janye "Naira darin Jonathan" daga yaduwa

- Sun koka kan cire larabcin ajami, wanda 'bashi da alaka da addini'

- An canja N100 ne a karshen 2014 don bikin murnar cikar Najeriya 100 da game kudu da arewa

Wata kungiyar musulmi, na so a sake canja fasalin Naira dari, ji dalilinsu

Wata kungiyar musulmi, na so a sake canja fasalin Naira dari, ji dalilinsu

Kungiyar kare hakkin musulmai ta bukaci Gwamnatin tarayya da ta hana yaduwar Naira dari saboda abinda ta kwatanta da "cire rubutun Ajami dake jikin kudin wanda Gwamnatin Goodluck Jonathan tayi a 2014.

A ranar talata ne shugaban kungiyar, farfesa Ishaq Akintola ya fadi hakan. Kungiyar ta kushe abinda tsohon shugaban kasar yayi hadi da cewa wannan babban ci baya a gwamnatin shi. A yayin da suka kwatanta sabon kudin da gwamnatin ta saka a 2014 da kaskantatta.

Kungiyar tayi kira da a maida rubutun Ajamin kuma a hana Naira 100 da 200 da gwamnatin Jonathan tayi yaduwa.

DUBA WANNAN: An saki wani bidiyo da bai yi wa Buhari dadi ba

"Gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ta fito da Naira dari don murnar cika shekaru 100 da fara buga kudi a Najeriya a ranar 19 ga watan Disamba, 2014. Abu mafi muni a kudin shi ne cire rubutun Ajami."

Su dai musulmi musamman na Arewa, sukan ga katsalandan ne idan aka taba addininsu ku al'adarsu, kuma sukan ga babu ruwan wani da rubutun ajami, duk da cewa yawancin masu amfani da kudin ya zuwa yanzu sun gane wacce ce wacce a nairas.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel