Shehu Sani ya nuna rashin jin dadinsa game da sace Sandar girma ta Majalissa
- Ciyaman na kwamitin majalissa na bangaren bashin gida dana waje, Sanata Shehu Sani ya nuna rashin jin dadinsa game da bacewar sandar girma ta majalissar
- Lokacin da DSP ikweremadu yake jawabi a majalissar wasu mutane biyar suka lababa suka sace sandar daga cikin majalissar
- Sanata Shehu Sani a shafinsa na Tuwita ya bayyana cewa majalisa bazata amince da irin wannan abun ba, yace nima na cire girman kai ina biyayya ga wannan Sanda inawa kasata aiki
Ciyaman na kwamitin majalissa na bangaren bashin gida dana waje, Sanata Shehu Sani ya nuna rashin jin dadinsa game da bacewar sandar girma ta majalissar a lokacin da ake zaman majalissar a ranar Laraba.
Dailytrust ta ruwaito cewa lokacin da DSP Ikweremadu yake jawabi a majalissar wasu mutane biyar suka lababa suka sace Sandar daga cikin majalissar, suna fita suka shiga wata babbar mota kirar Jeep suka gudu ta babbar kofar shiga harabar majalissar.
Sanata Shehu Sani a shafinsa na Tuwita ya bayyana cewa majalisa bazata amince da irin wannan abun ba, yace “nima na cire girman kai ina biyayya ga wannan Sanda inawa kasata aiki tare da abokanan aikina.”
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta bukaci a dawo da sadar iko cikin sa’o’i 24 bayan yan daba sun arce da ita
Sanata Shehu Sani ya nuna bacin ransa game da yanda za’a ce a cikin zaman majalissa ace har wasu mutane su iya shiga ciki su dauki Sandar girma ta majalissar su gudu da ita.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng