Yanzu-yanzu: Katapila ya fado kan motoci daga kan gada a Abuja

Yanzu-yanzu: Katapila ya fado kan motoci daga kan gada a Abuja

Labarin da muke samu yanzu daga majiya na bayyana cewa wani mumunan hadari ya far da safiyar yau Laraba, 18 ga watan Afrilu, 2018 a unguwan Karu, babban birnin tarayya Abuja.

Wannan abu ya faru ne yayinda wani katapila ya fado kan motoci daga kan gadan da aka fi sani da 'Karu Bridge' kusada unguwar Yanyan Abuja.

Katapilan ya fado kan motoci biyu amma; kirar Ford daya da kuma mota mai dauke da fasinjoji.

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa rundunar Yansandan kasar Indiya ta sanar da mutuwar wasu matafiya su 21 dake kan hanyar halartar bikin daurin auren dan uwansu a yankin Indiya ta tsakiya, inji rahoton jaridar Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito hatsarin ya faru ne a lardin Madhya Pradesh, da yammacin ranar Talata 17 ga watan Afrilu, yayinda motar ta wuntsulo daga samar gada, inda ta afka cikin wani tafku busashshe.

KU KARANTA:Yan biki su 21 sun gamu da ajalinsu a wani mummunan hatsari akan hanyar zuwa daurin aure

Wani babban jami’in Dansanda, Dilip Kumar ya bayyana cewa akalla mutane 29 sun jikkata ta hanyar samun rauni daban daban, inda yace da dama daga cikin wadanda abin ya shafa yan uwan Angon ne da suka nufi kauyen Pamari don daurin aurensa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel