Ba wanda zai damu da karanta labari na saboda katobarar da ake zargin na yi - IBB

Ba wanda zai damu da karanta labari na saboda katobarar da ake zargin na yi - IBB

Tsohon shugaban kasar Najeriya Ibrahim Babangida ya ayyana cewa shi yasan babu wani dan Najeriyar da zi dauki maganganun shi da muhimmanci musamman ma idan ya rubuta su saboda bakin fentin da yace an shafa mashi.

Janar Babangida dai yayi wannan bayanin ne a lokacin da ake fira da shi a gidan Talabijin din Channels inda aka tambaye shi ko zai rubuta tarihin sa a nan gaba musamman ma saboda ya fayyace wa jama'a babban dalilin da ya sa ya soke zaben 12 ga watan Yuni.

Ba wanda zai damu da karanta labari na saboda katobarar da ake zargin na yi - IBB
Ba wanda zai damu da karanta labari na saboda katobarar da ake zargin na yi - IBB

KU KARANTA: Za mu tabbatar Fayose yayi gidan yari - Ministan Buhari

Legit.ng ta samu dai cewa Janar IBB ya kuma kara da cewa yana rokon Allah ya ba wasu daga cikin matasan kasar nan daliban ilimi ko da a nan gaba ne su zauna su yi masa adalci musamman ma ganin cewa akwai muhimmin dalilin da yasa ya soke zaben.

A wani labarin kuma, Sabbin bayanai da ke fitowa daga hannun hukumar nan dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ta bayyana cewa shugaban jam'iyyar PDP Mista Prince Uche Secondus ya karbi Naira miliyan 250 daga hannaun Dasuki domin gudanar da wasu ayyuka na musamman.

Wannan dai kamar yadda muka samu na kunshe ne a cikin wani rahoton da hukumar ta kammala wanda kuma wakilin majiyar mu ya gani wanda aka kuma bayyana cewa ya anshi kudaden ne a gabanin gudanar da zabukan 2015.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel