Dubu ta cika: Yan sanda sun chafke masu garkuwa da Mutane su 4

Dubu ta cika: Yan sanda sun chafke masu garkuwa da Mutane su 4

- Kafin cafke masu garkuwa da Mutanen, sun karbi kudade a hannun mutane har N800,000

- Yanzu haka dubunsu ta cika, ana shirin gurfanar da su a gaban al'kali

Rundunar yan sanda reshen jihar Kebbi, tayi nasarar chafke wasu masu garkuwa da Mutane su hudu a karamar hukumar Koko- Basse. Haka-zalika rundunar tayi nasarar kwato kudade har Naira N800,000 da suka karba daga hannun Mutane.

Kakakin rundunar Yan sandan Jihar, DSP Mustapha Suleiman ne, ya bayyanawa manema labarai cewa, sun kamo masu garkuwar ne a wani sintiri da suka fita kan titin Koko-Basse- Fakai, bayan sun kammala ta’addancin nasu sun nufi karamar hukumar Zuru. “Wadanda ake zargin sune: Mohammadu Mani da Muhammadu Muhammad da Umar Mohammadu da kuma Abdulkarim Isiya”.

Dubu ta cika: Yan sanda sun chafke masu garkuwa da Mutane su 4
Dubu ta cika: Yan sanda sun chafke masu garkuwa da Mutane su 4

KU KARANTA: Zaben 2019: Abokanan Buhari ne basa fada masa gaskiya da suka ce ya nemi tazarce

“Duk kudaden da suka karba daga wurin wadanda suka fada komar tasu, munyi nasarar kwato su, kuma zamu mika su kotu domin su gurfna gaban al’kali”. Kakakin yan sandan ya fada.

Su dai masu garkuwa da mutanen, sun kama wani shugaban kabilar Fulani a yankin Koko-Basse mai suna Alhaji Aliyu Dikko, kuma har sun karbi Naira dubu dari uku (N300, 000) daga cikin miliyan uku da suka nema daga wurin iyalansa.

Haka- zalika wadanda ake zargin sun karbi karin wasu kudaden har Naira dubu dari biyar (N500, 000) daga wajen wani da suka kama, kafin dubunsu ta cika a cafke su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku

ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel