An kubutar da 'yan mata 19 daga arewa da ake kokarin safarar su zuwa kasar Saudiyya

An kubutar da 'yan mata 19 daga arewa da ake kokarin safarar su zuwa kasar Saudiyya

Hukumar nan ta gwamnatin tarayyar Najeriya mai alhakin hana safarar bil-adama ta National Agency for the Prohibition of Trafficking in Persons, NAPTIP a takaice ta sanar da samun nasarar kubutar da wasu 'yan matan arewa 19 da ake shirin yin safarar su zuwa kasar Saudiyya.

Hukumar ta NAPTIP ta ayyana cewa ta kai samame ne a wata unguwa dake a garin Abuja inda ake ta shire-shiren ficewa da su zuwa kasar ta Saudiyya.

An kubutar da 'yan mata 19 daga arewa da ake kokarin safarar su zuwa kasar Saudiyya
An kubutar da 'yan mata 19 daga arewa da ake kokarin safarar su zuwa kasar Saudiyya

KU KARANTA: Majalisar wakilai ta shirya binciken ministan Buhari

Legit.ng ta samu cewa matan wadanda 8 daga cikin su duk yara ne sun fito daga jihar Kano kuma ana kyautata zaton za a kai su Saudiyya din ne suyi aikatau ko karuwanci.

A wani labarin kuma, Hafsan sojojin kasa na Najeriya Laftanal Janar Tukur Buratai a ranar Alhamis din da ta gabata ya bayyana sake jadadda mubayi'ar sa ga shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari tare kuma da cigaba da yi masa biyayya hadi da kare demokradiyya.

Laftanal Janar Tukur Buratai wanda ya samu wakilcin Manjo Janar Rasheed Yusuf ya yi wannan kalamin ne a yayin da yake jawabi a wajen taron farkon watanni uku na shekarar 2018 na rundunar sojin kasar a Abuja.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng