Zargin kisan kai: Shehu Sani ya zargi El-Rufa’I da masa sharri, ya mayar da martini mai zafi

Zargin kisan kai: Shehu Sani ya zargi El-Rufa’I da masa sharri, ya mayar da martini mai zafi

Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisan dattawan Najeriya ya mayar da martini mai zafi bayan rahotanni sun yau cewa hukumar yan sandan Najeriya ta ambaci sunansa a cikin wadanda ake zargi da laifin kisan kai.

Hukumar yan sanda ta saki jawabin cewa ana zargin sanatan da hannu cikin wannan harin kisan kai a jihar Kaduna bisa ga wani jawabin kaset da aka ji.

Kwamishanan yan sandan jihar Kaduna ya rubuta wasikan bukatan ganin sanatan ranan 30 ga watan Afrilu a shelkwatan hukumar na jihar Kaduna domin bayani da bincike.

Zargin kisan kai: Shehu Sani ya zargi El-Rufa’I da masa sharri, ya mayar da martini mai zafi
Zargin kisan kai: Shehu Sani ya zargi El-Rufa’I da masa sharri, ya mayar da martini mai zafi

Da jin wannan rahoto, sanatan ya mayar da martini mai zafi inda ya zargi gwamnan jihar Kaduna da kulla masa sharri. A jawabinsa, Shehu Sani yace:

“Yinkurin da gwamnan Kaduna Nasiru Elrufai yake yi na kulla mani sharri tare da hannun Yan’Sanda ba zai ci nasara ba. Na Sami Labarin kulle kulle da yake yi. Sharri dan aike ne ko ka tura shi zai dawo maka. Ina mai Sanar da Nasiru cewa Wannan sharrin,Kaman na baya da yayi ba zai hana ni kalubalantar azzaluman gwamnati da yake shugabanci a Jahar Kaduna ba.”

KU KARANTA: Hukumar 'yan sanda ta aikewa Sanatan Shehu Sani sammaci bisa zargin kisa

Rikici tsakani Gwamna Nasir El-Rufa’I da Sanata Shehu Sani ya fara ne tun wani sabani da suka samu a farin gwamnatin APC a 2015. Har yanzu an gaza sulhu tsakaninsu bal rikicin kara zurfafa ya keyi

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng