Zaben kananan hukumomi: Jam’iyyar APC ta kama da wuta a Kaduna

Zaben kananan hukumomi: Jam’iyyar APC ta kama da wuta a Kaduna

- Zaben fidda yan takarar kanann hukumomin jihar Kaduna ya bar baya da kura.

- Jam’iyyar APC kuma tace bata san wannan zance ba

Wasu yan takarar kasiloli a jam;yyar APC a jihar Kaduna sun gudanar da zanga-zangar limana, domin abinda suka kira magudin zaben na cikin gida yayi zaben fidda gwani gabanin zaben kananan hukumomin Jihar.

Zaben kananan hukumomi: Jam’iyyar APC ta kama da wuta a Kaduna
Zaben kananan hukumomi: Jam’iyyar APC ta kama da wuta a Kaduna

Yan takarar sunce zaben cikin gidan na fidda gwani da aka yi shi ranar 29 ga watan da ya gabata, anyi danniya a cikinsa.

Masu zanga-zangar dai sun ke waye shataletalen Lord Lugard inda ofishin jam’iyyar yake, suna dauke da kwalaye da ajikinsu aka rubutan “Rashin adalci barazana ne ga wanzuwar al’ummah. Abin takaici ne bayan munyi aiki tukuru ga jam’iyyarmu ayi mana irin wannan rashin adalcin.” A cewar masu zanga-zangar.

Da yake shaidawa manema labarai, shugaban kungiyar yan takarar kansilolin na karamar hukumar Kaduna ta Arewa, Aminu Adam yace, sunyi zanga-zangar ne domin nunawa gwamnan jihar Nasir El-Rufai da shugabancin APC na jihar irin bacin randa da suke ciki.

KU KARANTA: Tarihin kasuwanci da rayuwar ‘Dan kasuwan Duniya Aliko Dangote

Yace, jawabin da gwamnatin jihar ta fitar ne cewa zata bari ayi zabe ba tare da katsa landan ba, yasa suka sami kwarin gwuiwar fitowa takarar domin suna tsammanin adalci. Amma sai dai kash wasu manyan yan siyasa a jihar sunki bin waccan hanya da gwamnan yayi alkawari inda suka yi katsa landan a cikin harkokin zaben yayin gudanar da shi. Kamar yadda rahoton Premiun Times ya tabbatar.

“Katsalandan din da su kayi ya fito fili har ta kai ga kowa ya gane abinda suke shiryawa,na kin barin zabe ya gudana a mazabu 12 na karamar hukumar Kaduna ta Arewa kamar yadda aka shirya.” Adam ya tabbatar

Ya kuma cigaba da cewa, “Shirun da suka ji gwamnatin jihar da sauran hukumomin da abin ya shafa suka yi ne ya sanya dole suka fito domin gudanar da zanga-zangar lumanar, domin a magance matsalar da ka iya zama barazana ga hadin kan jam’iyyar a jihar ko ma ya zama sanadiyyar faduwar jam’iyyar zabe”

Daga cikin magudin da aka shirya har da rashin samar da kayan aikin gudanar da zabe kamar; takardar kada kuri’a da akwatin sanya kuri’un da aka kada, da rigistar dake kunshe da sunan duk yan jam’iyya. A cewar Aminu Adam.

A saboda haka ne yayi kira ga gwamnan jihar da shugabannin jam’iyyar da su kawo dauki wajen magance rigimar cikin gidan da ta dabaibaye jam’iyyar.

‎Koda majiyarmu ta tuntubi mukaddashin sakataren Jam’iyyar ta APC na jihar Kaduna, Yahaya Pate, ya shaida mana cewa, su dai a iya saninsu an gudanar da sahihin zabe a dukkan kananan hukumomin jihar 23.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng