Hukumar 'yan sanda ta bankado wata makerar makamai a jihar Neja, karanta jerin makaman da suke kerawa

Hukumar 'yan sanda ta bankado wata makerar makamai a jihar Neja, karanta jerin makaman da suke kerawa

Hukumar 'yan sanda a jihar Neja ta bankado wata haramtacciyar masana'antar kera makamai a karamar hukumar Mashegu dake jihar.

An samu bindigu na musamman 110 da suka hada da kananun bindigu, bindigar gida samfurin AK 47 da bindiga mai sarrafa kanta da kuma alburusai masu yawa.

Hukumar 'yan sanda ta bankado wata makerar makamai a jihar Neja, karanta jerin makaman da suke kerawa
Miyagun makamai

Da yake jawabi ga manema labarai yayin gabatar da makaman, kwamishinan 'yan sandan jihar, Mista Paul Dibbal, ya bayyana hukumar ta samu rahoton cewar wasu mutane na kera makamai, kuma suka bi sahu ta hanyar amfani da dabarun aiki har ta kai ga sun yi nasarar cafke wadanda ke gudanar da muguwar sana'ar.

DUBA WANNAN: Matsin lamba ya saka Buhari bayyana kara tsayawa takara - Gwamna Shettima

Ya kara jaddada cewar hukumar 'yan sanda na aiki da umarnin babban Sifeton hukumar, Ibrahim Idris, domin tabbatar da makamai sun bar hannun farar hula.

Ya shawarci duk wani mutum ko kungiya dake da makamai da su mika su hannun hukumar 'yan sanda kafin wa'adin da hukumar ta diba ya kare, wanda daga nan duk wanda aka kama da mallakar makami ba bisa ka'ida ba zai fuskanci fushin hukuma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel