Maganganun da Annabi Isa ya fada min a lokacin da ya bayyana a gareni har sau 4 – Inji wata Mata
Wata Mata mai suna Ramotu Audu, ma’abociyar kafar sadarwa zamani ta Facebook ta bayyana ma mabiyanta a shafinta cewar sau hudu tana yin arba da Anna Isa Almasihu a cikin mafarkinta.
Jaridar Ebira reporters ta ruwaito matar yar asalin jihar Kogi ta nemi mabiyanta a shafin da su taimaka mata da amsar wannan mafarke mafarke da take yi, kamar yadda Legit.ng ta jiyo.
KU KARANTA: Sharrin Almajiranci: An tsinci gawar wani Almajiri bayan an farke masa ciki a garin Katsina
Ramotu ta ce: “Ni fa cikakkiyar Musulma ce, amma Annabi Isa ya bayyana a cikin mafarkina fiye sau hudu, yace zai cece ni, na tambayesa a mafarkin da na yi na yau cewa mai yasa zai cece ni, sai ya nuna min wasu mutane, ya umarce ni da nayi musu addu’a, zasu samu albarka.
“Amma fa ina bude bakina da nufin zan fara addu’a ga mutanen sai kawai na farka daga wannan barci, jama’a ku bani shawara, don kuwa n agama rikicewa.” Inji ta.
A wani labarin kuma an samu wata mata a jihar Bauchi da ta haifi jariri dauke da Qur’ani, har ma da carbi, inda wasu rahotanni suka nuna uwar yaron ta kai shi wajen Shehu Dahiru Bauchi, wanda yayi masa addu’a.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng