Namu ya samu: Buhari ya ware Naira miliyan 100 don gyaran hanyar Kano-Gwarzo-Dayi

Namu ya samu: Buhari ya ware Naira miliyan 100 don gyaran hanyar Kano-Gwarzo-Dayi

Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ayyana ware kimanin makudan kudaden da suka kai Naira miliyan 100 domin aiwatar da gyaran hanyar da ta tashi daga Kano ta nufi Gwarzo har zuwa Dayi na karamar hukumar Malumfashi, jihar Katsina.

Shugaban hukumar nan dake yin ayyukan gyaran hanyoyi ta gwamnatin tarayya watau Federal Road Maintenance Agency (FERMA) na shiyyar Kano Injiniya Adedayo Adebayo shine ya sanar da hakan ga manema labarai a ranar Alhamis.

Namu ya samu: Buhari ya ware Naira miliyan 100 don gyaran hanyar Kano-Gwarzo-Dayi
Namu ya samu: Buhari ya ware Naira miliyan 100 don gyaran hanyar Kano-Gwarzo-Dayi

KU KARANTA: Amarya ta yi shagalin bikin ba-zata a jihar Bauchi

Legit.ng dai ta samu cewa Injiniya Adedayo Adebayo ya kuma kara da cewa yanzu dai tuni har hukumar ta kammala shire-shiren bayar da kwangilar gyaran hanyar mai tsawon kilomita 125 da ta hada jihar ta kano da sauran takwarorin ta na Katsina Sokoto, Kebbi da ma jamhuriyar Niger.

A wani labarin kuma, Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari a ranar Alhamis din nan a fadar sa dake a garin Abuja ya ayyana cewa shi fa gwamnatin da yake shugabanta ba ta da buri ko kudurin taimako ko kuma fifita wani addini a kasar nan.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a yayin da ya karbi bakuncin shugabannin addinin Kirista daga yankin arewacin Najeriya dake da rajin tabbatar da samuwar zaman lafiya karkashin jagorancin Bishop John Abu Richard.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel