Jam’iyyar PDP tayi babban asara a jihar Yobe inda mambobinta 7000 suka koma jam’iyyar APC
- Babbar asara ta samu jam’iyyar PDP, inda mutane 7000 suka bar jam’iyyar a karamar hukumar Pataskum
- Jagoran wadanda suka bar jam’iyyar, Alhaji Ibrahim Saleh Jauro, yace jam’iyyar ta rabu biyu a karamar hukumar
- Jigon jam’iyyar APC Alhaji Ibrahim Bomai, wanda ya karbi bakuncinsu zuwa tasu jam’iyyar yace a shirye yake da kara karbar bakuncin masu son cigaban yankin
Babban asara ta samu jam’iyyar PDP, inda mutane 7000 suka bar jam’iyyar a karamar hukumar Pataskum.
Jagoran wadanda suka bar jam’iyyar, Alhaji Ibrahim Saleh Jauro, yace jam’iyyar ta rabu biyu a karamar hukumar inda kowa ke kokarin tsaida nashi dan takarar daban a zaben 2019.
Jigon jam’iyyar APC Alhaji Ibrahim Bomai, wanda ya karbi bakuncinsu zuwa tasu jam’iyyar yace a shirye yake da kara karbar bakuncin masu son cigaban yankin na zone B da jihar ta Yobe baki daya.
"APC tayi farin ciki da kuka gane gaskiya, wanda hakan na nuna abubuwan kirki da gwamnan jihar ta Yobe, Ibrahim Gaidam yakeyi”, inji shi.
KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta bayyana sunaye da kudaden data karba daga hannun wadanda suka dibi kudaden al’umma – Timi Frank
Ya kumayi jinjina ga gwamnan jihar Ibrahim Gaidam, bisaga cigaban daya kawo wanda shine makasudin janyo hankalin ‘yan jam’iyyar adawa su dawo tasu jam’iyyar ba tare da fargaba ba.
Haka zalika shugaban matasa na jam’iyyar PDP a karamar hukumar ta Pataskum, Alhaji Lamaran yace sun bar jam’iyyar ne don biyayya ga Alhaji Ibrahim Bomai.
Hajiya Hauwa’u Ibrahim Nagodi, shugabar mata ta jam’iyyar PDP, ta bayyana Bomai a matsayin shugaba mai adalci da son cigaban da taimakon al’umma na jihar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng