'Yan shi'a suna da cikakken 'yanci a Saudiyya kamar kowa - Yarima Mohammed bin Salman
Yayin da kasar Saudiyya ke ta dada kara shiga cikin cakwakiyar rikicin addini sakamakon kokarin kawo sauye-sauye a kasar da Yarima Mohammed bin Salman ke yi, ya bayyana cewa shi a kasar sa yanzu babu sauran banbanci a tsakanin 'yan Shi'a da 'yan Sunni.
Yariman yayi wannan ikirarin ne a lokacin da yake fira da wata jaridar Atlantic a nahiyar turai inda yake ziyarar aiki tun satin da ya shude.
KU KARANTA: Saraki ya karyata rade-raden fitowar shi takara
Legit.ng ta samu cewa Yarima Mohammed bin Salman ya bayyana cewa shi yayi ammana cewa akwai 'yan shi'a a kasar ta Makka sannan kuma akwai 'yan Sunni wadanda suma sun rarrabu zuwa kusan kashi hudu kuma dukkan su suna da damar da za su yi addinin su ba tare da tsangwama ba.
A wani labarin kuma, Sakamakon kokarin samar da sauye-sauye a bangaren dodkin kasar daular musulunci ta Saudiyya, Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ya bayyana kudurin gwamnatin masarautar kasar na bude wajen shakatawa na musamman inda mata za su iya yawon su a tsirara.
Sai dai mun samu cewa masarautar ta bayyana cewa wannan wajen zai zama kebantacce ne ta yadda mata ne kadai za su je wajen kuma a wurin za su iya saka kayan wanka ba tare da sun rufe jikin su ba.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng