Barayin gwamnati: Jam'iyyar PDP ta mayarwa da Buhari martani

Barayin gwamnati: Jam'iyyar PDP ta mayarwa da Buhari martani

Jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta bayyana jerin mutanen da gwamnatin APC ta wallafa da sunan cewa barayi ne a matsayin karya da soki-burutsu tsagwaron sa.

Haka zalika jam'iyyar ta PDP ta kuma bayyana cewa an zayyana sunayen wasu daga cikin jiga-jigan ta ne kawai domin a bata masu suna duk kuwa da cewa wasu daga cikin su duk maganar su na a gaban kotu.

Barayin gwamnati: Jam'iyyar PDP ta mayarwa da Buhari martani
Barayin gwamnati: Jam'iyyar PDP ta mayarwa da Buhari martani

KU KARANTA: Muhadu a kotu - Uche Secondus ya shaidawa Lai Mohammed

Legit.ng ta samu cewa daga nan ne ma dai sai jam'iyyar ta PDP ta bukaci dukkan 'yan Najeriya da su yi fatali da zancen domin kuwa har yanzu babu wanda kotu ta tabbatar da ya dauki koda sisin kwabon jama'a kamar yadda suka fada.

A wani labarin kuma, Shugaban jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), mai suna Prince Uche Secondus ya fadawa babban ministan yada labarai da kuma habaka al'adu na gwamnatin tarayyar Najeriya Alhaji Lai Mohammed cewar ya shiraya jiran sammacin kotu.

Uche Secondus ya bayyana cewa ko shakka babu ba zai bar kazafin da yayi masa ba na cewa ya wawuri kudin al'ummar Najeriya da suka kai Naira miliyan 200 ya tafi a banza ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel