Kamfanin rodi na Ajaokuta zai sami dala biliyan daya domin tayar dashi daga majalisar wakilai
- Shekaru talatin kenan ana antaya wa kamfanin rodi na Ajaokuta a Kogi kudade
- An sha sayar dashi amma gwamnatoci na karbowa
- Za'a ciro dala biliyan daya daga rarar mai a baiwa kamfanin domin ayyukansa su bunkasa
Majalisar wakilai ta sahalewa gwamnatin Tarayya ciro kudi da suka kai dala biliyan daya, watau akalla NAira biliyan 365 domin a kashe kan babban kamfanin rodi na kasa na Ajaokuta wanda yake jihar Kogi kuma yake bukatar kudaden tayar da komadarsa.
Shi dai kamfanin na rodin, ya shekara akalla talatin da kaffuwa, kuma akwai hasashen zai iya samar wa da dunia rodi da zai kawo wa kasar nan babbar riba.
Sai dai shekaru da yawa bayan assasa kamfanin, ya sha kalubale da ma tsufan kayan aiki, da gwamnatoci suka yi tayi dashi, musamman sakaci da rashin kudi da ma kasa iya tafiyyar da babbar masana'anta haka a Najeriyar.
DUBA WANNAN: Tecno zai bude kamfani a Najeriya saboda kasuwar da yake samu
Yanzu dai majalisar tace wadannan kudade za'a yi amfani dasu ne domin farfado da kamfannin, domin dawo da martabarsa, samar da aikin yi, samar da rodi, wutar lantarki da ma ciyar da tattalin arzikin kasar nan gaba.
Za'a ciro kudin ne daga biliyoyin daloli da kasar nan ta tara daga ribar mai, ta ajiye a kasar waje domin shiriin ko ta kwana kan farashin mai, tsaro, da ayyuka na musamman.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng